Bayern Munich Bazata tsagaita wuta akan Aroujo ba.

Bayern Munich ba ta daina zawarcin dan wasan bayan Barcelona Ronald Araujo, ba inda Sky Sports Deutschland ta ruwaito cewa Kungiyar a shirye take ta bayar da sama da Yuro miliyan 70 domin daukar dan wasan.
Sai dai bayanin ya kara da cewa ko da yuro miliyan 80 Kungiyar zata bayar ba zai samu karbuwa ba a lokacin kasuwar musayar 'yan wasa ta watan Janairu, inda Barça ke son rike dan wasan na Uruguay.

Kudin fansar kwantiragin dan wasan Yuro billion 1 ne amma Bayern ta yi imanin cewa Barça za ta iya barinshi ya tafi idan suka samu kudi Mai kyau domin samun kudin zai taimakawa matsalolin kuɗin da suke ciki.

Ta bangaren Barcelona kuwa Matsayarsu a koyaushe itace baza su saurari tayin siyar da dan wasan ba, Amma Bayern Munich Sun yi imanin Araujo zai iya canza tsaron bayan Kungiyar su kamar yadda Kane ke zura kwallaye tun bayan da ya koma Kungiyar daga Tottenham Hotspur.
KUNDIN WASANNI SHAFIN LABARAN WASANNI LAMBA 1 A AFRIKA https://kundinwasannee.blogspot.com/
Older Posts Older Posts

Comments

Post a Comment