Barcelona zata dauki Messinho

Jaridar Mundo Deportivo ta rawaito cewa Barcelona a shirye take ta dauki matakin ganin ta dauki dan wasa Estevao Willian daga Palmeiras.
Estevao yana da shekaru 16 kacal ba a ba shi damar komawa Barcelona a hukumance, kuma dole ne ya jira har sai ya cika shekaru 18 a watan Afrilun 2025 - ma'ana zai iya komawa Spain a farkon kakar 2025-26.

Barca na da sha'awar cimma yarjejeniya daukar dan wasan, kuma rahoton ya ce da tuni sun yi hakan amma saboda takunkumin da suke ciki na kudi shine ya Basu tsaiko akan daukar dan wasan.

Duk da haka, dan wasan wanda ake yi wa lakabi da "Messinho," - ya ba da gudummawa ga komawa Barca, wanda ya ba wa kulob din Catalan lokaci don tsara shawarar yadda zasu daukesa Kungiyoyi irinsu Arsenal, Chelsea, Manchester City, Manchester United da Paris Saint-Germain duk suna son daukasa. .

Rahotan yaci Gaba da cewa Kungiyar Palmeiras na da niyyar mutunta hukuncin Estevao Kuma zasu jira Barca, wacce ke ganin shi a matsayin dan takarar lashe kyautar Ballon d’Or a nan gaba.
KUNDIN WASANNI SHAFIN LABARAN WASANNI LAMBA 1 A AFRIKA https://kundinwasannee.blogspot.com/?hl=ar
رسائل أحدث رسائل أحدث رسائل أقدم رسائل أقدم

المزيد من المشاركات

تعليقات

إرسال تعليق